‘Yan bindiga sun sake kaddamar da hari a Libya
Rahotanni daga kasar Libya sun ce ‘Yan bindiga sun sake kaddamar da sabbin hare hare a tashar jiragen saman birnin Tripoli kwanaki biyu bayan yunkurin tattaunawar zaman lafiya ya ci tura. Wani jami’in tashar jiragen saman Al Jilani Al Dahesh yace an kai hare haren na yau ne da rokoki da bama bamai da kuma tankin yaki.
Wallafawa ranar:
Ko a ranar juma’a, Libya ta bukaci taimakon Majalisar Dinkin Duniya wajen kare tashoshin jiragen sama da kuma rijiyoyin mai.
Rahotanni sun ce mutum guda ya rasa ransa a fadan tsakanin mayakan Zintan da ke gwagwarmaya tare da wasu mayaka don kafa gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu