Isa ga babban shafi
Libya

Libya ta nemi taimakon MDD

Kasar Libya ta nemi taimakon Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya taimaka da rundunar tsaro saboda yadda al’amurran tsaro ke ci gaba da sukurkucewa a kasar. Ministan harakokin wajen kasar Mohammad Abdelaziz ya bukaci a aiko da kwararru da za su horas da dakarun kasar domin samar da kariya ga cibiyoyin Mai a kasar.

Hayaki ya turmuke sama a birnin Tripoli na Libya
Hayaki ya turmuke sama a birnin Tripoli na Libya
Talla

Daga cikin muhimman wuraren da hukumomi a kasar Libya ke bukatar a samarwa kariya sun hada da Tsibirran da ake hakar danyen Man Fetir da filayen jiragen kasar da dai sauransu.

Mohammad Abdelaziz ya ce ba suna bukatar hukumomin kasa-da-kasa su yi kaka-gida ne a cikin kasar kamar a wasu kasashe ba, illa suna bukatar kwararru ne daga Majalisar dunkin Duniya kan sha’anin tsaro.

Libya dai na ta fama ne da tashe-tashen hankula a ‘yan kwanakin nan a yayin da ‘yan tawaye masu tayar da kayar-baya ke ta fafatawa kusa da filin jirgin Tripoli a wani yanayi da ke son jefa kasar ga yakin basasa.

Yanzu haka dai ana sa ran Mambobi 15 na kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya za su gabatar da wani rubutaccen jawabi akan kasar ta Libya. Kodayakea Majalisar Dinkin Duniya ta kwashe ma’aikatanta a Makon jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.