Isa ga babban shafi
Libya

An kashe mutane 8 a wani sabon fada a Bengazi Libya

Wani Sabon fada a Bengazi da ke kasar Libya tsakanin magoya bayan Janar Khalifa Haftar da wasu ‘Yan tawayen kasar, ya yi sanadiyar kashe akalla mutane 8 yayin da wasu 15 suka samu raunuka

telegraph.co.uk
Talla

Rahotanni sun ce fadan na daya daga cikin mafi muni da mutanen garin suka gani, tun bayan lokacin da magoya bayan Janar din suka dauki makamai, tare da kai farmaki ga wasu ‘yan tawaye kamar su, a wani farmakin da suka yiwa suna da Operation Dgnity a turance ranar 16 ga watan Mayu lokacin da aka ce akalla mutane 76 sun bakunci Lahira.

Kasar Libya dai ta fada cikin tashin hankalin tun bayan kashe tsohon shugaban kasar Mu’ammar Ghadafi, a wani bore da kassahen yammacin Duniya suka jagoranta.

Tun a wannan lokacin ne dai al’ummar kasra suka shiga halin damuwa bayan da Makmai suka yawaita a cikin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.