Isa ga babban shafi
Kenya

Soji sun kona sansanin ‘yan sanda da Gidaje da Motoci a Kenya

A kasar Kenya wasu yan bindiga sun kai hari barikin ‘yan sanda tare da kona gidaje da kuma lalata dukiyoyin al’umma. Wannan kuwa na faruwa ne a daidai lokacin da rikicin kasar ke kara kamari

usatoday.com
Talla

Sakamakon faruwan wannan harin dai, daruruwan mutane sun tsere wa gidajensu da ke yankin Lamu inda al’amarin ya fi kamari.

Harin na ranar talata da aka kai a Barikin ‘yan sanda ya biyo bayan wani kazamin hari da aka kai ranar asabar da ta gabata da ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane akalla 9.

Yanzu haka dai jama’a na zama cikin fargaba sakamakon wasu takardu da aka lilika jikin Bishiyoyi da ke yiwa kristoci da gwamnati gargadi su daina matsawa musulmin kasar, sai dai kuma babu bayani a takardar ko me yin hakan zai haifar.

Duk da cewa ana danganta wadanan hare-haren akan kungiyar nan ta al-shebab mai alaka da kungiyar al-Qaeda gwamnatin kasar Kenya ta karyata zargin da ake cewa siyasa ce kurum.

Gwamnati dai ta sha alwashin gano wadanda suke kai hare haren tare da kawo karshen tashe-tashen hankulan da kasar ta Kenya ke fuskanta a baya bayan nan
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.