‘Yan bindiga sun kashe mutane da dama a Kenya
Akalla mutane 29 aka tabbatar da mutuwarsu a wasu hare hare da ‘Yan bindiga suka kai a wasu yankuna gudana biyu a kasar Kenya, kamar yadda mahukuntan kasar suka tabbatar. ‘Yan sanda sun zargi wasu ‘Yan a ware a kasar duk da Mayakan Al Shabaab na Somalia sun yi ikirarin daukar alhakin kai hare haren.
Wallafawa ranar:
Ma’aikatar cikin gida tace mutane Tara aka kashe a harin da aka kai a yankin Lamu a ranar Assabar, kusa da inda aka taba kashe mutane sama da 60 a wani hari da aka kai a watan jiya.
Mutane 20 ne kuma aka kashe a wani hari da aka kai a ofishin ‘Yan sanda a Gamba da ke yankin Tana River County.
‘Yan sanda sun zargi kungiyar ‘Yan a ware ta Mombasa Republican Council, amma kungiyar Al Shabab tace ita ce ta kai hare haren.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu