Isa ga babban shafi
Kenya-Somalia

Kenyatta ya dora alhakin hare hare kan ‘yan siyasa

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya karyata rahotannin da ake fitarwa cewar kungiyar al-Shabab ce ta shirya hare haren da aka kai a baya-bayan nan a kasar, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta
Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta Kenyagvt
Talla

Kenyatta ya dora alhakin harin ne kan ‘yan Siyasar masu hamayya da shi.

“Harin da aka kai a Lamu, shirya shi aka yi, kuma duk kulle-kullen ‘yan siyasa ne da ke kokarin kitsa tashin hankalin kabilanci a tsakanin mutanen Kenya.” In ji Kenyatta.

Kenyatta har ila yau kara da cewa “An tattara bayannai akan harin da aka kai wa jami’an tsaro a Mpeketoni, amma Jami’an tsaro basu yi komai akai ba.”

Wadanan kalamai na Kenyatta na zuwa ne duk da cewa kungiyar ta Al Shabab ta dauki alhakin kai wadanne hare hare.

Kungiyar ta ce hare haren daukar fansa ne kan yadda dakarun Kenya suka mamaye wasu yankunan Somaliya da kuma yadda ake muzgunawa Musulman kasar ta Kenya.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.