Isa ga babban shafi
Kenya

Harin da aka kai kasar kenya ya hallaka mutane 49

Wasu ‘Yan Bindiga da ake zaton Yan kungiyar Al-Shebaab ne sun bude wuta a wani hari da suka kai a garin Mpeketoni da ke kusa da Mombasan kasar Kenya, inda suka kashe mutane 49

georgianewsday.com
Talla

Benson Maisori, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda na yankin, ya ce sun kwashe gawawaki 26 kai tsaye bayan kai harin, amma suna ci gaba da kewaye inda aka kai harin ko za su samu wasu.

Kungiyar Al-Shebaab dai ta dade tana kai hare-hare a kasar Kenya saboda abinda ta kira ramuwar gayya akan mamayen da sojin kasar suka yiwa kasar Somalia.

Akalla dai maharan 50 ne suka zo dauke da muggan makamai suka kuma kutsa birnin Mpeketoni da ke kusa da tsibirin Lamu, bagiren da ke jan hankalin masu yawon bude Ido.

Wata mazaunyar yankin Anne Gathigi mai shekaru 38 Uwar Yara 5 ta tabbatarwa Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewar maharan sun kashe mata Miji.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.