Isa ga babban shafi
Kenya-Somalia

Al Shabab ta kai hari na biyu a Kenya

Akalla mutane 15 ne suka rasa rayukansu, bayan wani sabon hari da aka kai a wani yanki dake gabar tekun kasar Kenya. Wannan lamari ya faru ne kasa da sa’oi 24, bayan harin da kungiyar Al Shabab ta kai, wanda ya hallaka mutane kusan 50.  

Wani bangare da 'yan kungiyar Al Shabab suka kai hari a Kenya
Wani bangare da 'yan kungiyar Al Shabab suka kai hari a Kenya REUTERS/Joseph Okanga
Talla

Kungiyar Al Shabab wacce ake alakantawa da kungiyar Al Qaeda dake da tushe a Somaliya, ta ce ita takai wannan hari a karo na biyu, wanda ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan sanda da masu tsoron lafiyar namun daji a wasu wuraren shkatawa.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce ta samu nasarar kai wadannan hare hare kuma mayakanta sun koma gida lafiya.

Rundunar ‘Yan sanda a kasar ta Kenya, ta bayyana cewa mutanen da suka kai harin na baya baya nan, sune suka kai harin farko a garin Mpeketoni, wanda ya halaka mutane 49.

Kakakin ‘rundunar ‘yan sandan ta kuma ce an kai harin ne yayin da hukumomin tsaro ke kokarin tura karin dakaru zuwa yankin domin samar da cikakken tsaro.

Dama dai kungiyar ta Al Shabab, ta yi gargadin ci gaba da kai hare hare, wanda ta ce daukan kan fansa ne kan yadda dakarun Kenya suka mamaye wasu yankunan Somaliya da kuma yadda ake muzgunawa Musulmai a Kenyar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.