Isa ga babban shafi
Uganda

Mutane 50 sun mutu a rikicin Uganda

Akalla mutane 50 ne suka rasa rayukansu, akan iyakar kasar Uganda da Jamhuriyar Dimokradiyar Congo, bayan da dakarun kasar ta Uganda suka yi wata arangama da wasu mayaka.

Taswira da Tutar kasar Uganda
Taswira da Tutar kasar Uganda
Talla

Babu bayanai da ke nuna kai tsaye ko me ya haifar da fadan, amma yankin Yammcin kasar, yanki ne, da ya sha fama da fadan addini da kabilanci.

Kakakin dakarun kasar Uganda, Padd Ankunda, ya gayawa Kamfanin Dillancin labaran Faransa cewa, wasu mutane dauke da makamai ne suka abka cikin barikin soji da ke wani wuri da ake kira Bundibugyo suna ta harbi, lamarin da ya sa Sojojin suka mayar da martani.

Kodayake Kakakin yace mutane 41 ne suka rasa rayukansu a arangamar, Amma wata jaridar kasar Uganda da ake kira New Vision ta ruwaito cewa wadanda aka kashe sun haura mutane 50.

Sojin kasar da ‘Yan sanda sun kuma musanta zargin da ke cewa fadan na da alaka da wata kungiyar mai tayar da kayar baya, suna masu danganta rikicin da na kabilanci da addini.

Yanzu haka rundunar sojin kasar tace mutane uku daga cikin maharan suna hannunsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.