Isa ga babban shafi
Congo-Uganda

Uganda ta ki mika wa Congo 'Yan tawayen M23 da suka mika kai

Ma’aikatar tsaron kasar Uganda tace ba za ta mika wa Jamhuriyyar Dimokuradiyar Congo ‘Yan tawayen M23 ba wadanda suka tsere zuwa kasar bayan dakarun Sojin Congo sun samu galaba akansu, kamar yadda kakakin ma’aikatar tsaron kasar ya tabbatar.

Des ex-rebelles présumés regroupés après s'être rendus à l'armée congolaise, dans le village de Chanzo, non loin de Goma le 5 novembre 2013.
Des ex-rebelles présumés regroupés après s'être rendus à l'armée congolaise, dans le village de Chanzo, non loin de Goma le 5 novembre 2013. REUTERS/Kenny Katombe
Talla

Kanal Paddy Ankunda ya shaidawa Kamfanin Dillacin Labaran Faransa cewa hakkinsu su ne su kare ‘Yan tawayen domin ba fursunoni bane illa Sojoji da suka gujewa yaki a kasarsu.

Mista Ankunda ya kara da cewa Uganda ta tarbe su hannu biyu kamar yadda ta tarbi dakarun Gwamnatin Uganda da suka gujewa yaki a farkon shekarar nan.

‘Yan tawayen M23 da dama ne da ke yaki a Jamhuriyyar Congo suka mika kai a kasar Uganda cikinsu har da Kwamandansu Sultani Makenga, bayan dakarun Congo sun samu nasara akan su.

Hakan ke nuna an kawo karshen rikicin kasar Jamhuriyyar Congo da aka kwashe tsawon watanni 18 ‘Yan tawayen M23 suna addabar kasar.

Paddy Ankunda, yace  kimanin ‘Yan tawayen 1,500 ne suka mika kai bayan sun tsallako daga Congo.

Sai dai kuma Kanal din na Sojin Uganda yace babu tabbacin ko Makenga yana cikin tawagar ‘Yan tawayen na M23 da suka mika kai.

Uganda da ke makwabtaka da Jamhuriyyar Dimokuradiyar Congo ta fuskanci suka daga Majalisar Dinkin Duniya akan tana taimakawa ‘Yan tawayen M23, al’amarin da gwamnatin Kampala ta musanta.

Makenga mai shekaru 39, tsohon Kanal din Sojin Jamhuriyyar Congo ne wanda ake zargi da aikata laifukan yaki da suka shafi kisa da fyade da kuma tursasawa kananan yara shiga aikin Soji, wanda kuma ke fuskantar takunkumin Amurka da Majalisar Dinkin Duniya.

Yanzu haka Dakarun Congo sun kori ‘Yan tawayen na M23 a yankunan da suka mamaye a arewacin Kivu mai arzikin ma’adinan kasa.

An fara samun rikicin ‘Yan tawayen M23 ne a ranar 23 ga watan Maris a shekarar 2009 wadanda suka samo asali daga ‘Yan tawayen Tutsi kafin su koma dakarun Congo.

Amma a shekarar 2012 ‘Yan tawayen suka balle daga yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla, suna masu zargin gwamnatin kasar da rashin cim ma bukatunsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.