Isa ga babban shafi
Uganda

Uganda ta yi watsi da takunkumin Amurka

Gwamnatin kasar Uganda tace babu wani tasiri da takunkumin Amurka zai yi akanta sakamakon dokar hana madigo da Luwadi da aka kafa a kasar, tare da yin watsi da zargin ana cin zarafin mutane a cikin kasar  da sunan farautar nasu auren jinsi guda.

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni yana sanya hannu kan dokar haramta Luwadi da Madigo
Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni yana sanya hannu kan dokar haramta Luwadi da Madigo Reuters/James Akena
Talla

Amurka ta sanya wa kasar Uganda takunkumi, sakamakon dokar haramta luwadi da madigo da aka sanya a kasar, inda hukumomin Washington suka ce dokar zata take hakkin dan Adam.

Takunkumin ya hada da dakatar da duk wani hadin gwiwar ayyukan soja tsakanin kasashen, tare da hana bayar da izinin shiga Amurka ga wasu jami’an gwamnatin Uganda.

Dokar, da shugaba Yoweri Museveni ya sanya wa hannu, ta bayar da damar aiwatar da daurin rai da rai ga duk wanda aka samu yana yi ko goyon bayan masu aikata luwandi da Madigo.

Kakakin gwamnatin Uganda Ofwono Opondo yace suna iya dogaro da kansu ba tare da tallafin Amurka ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.