Isa ga babban shafi
Uganda

Shugaban kasar Uganda ya yi gargadi akan cutar Ebola

Shugaban Kasar Uganda, Yoweri Museveni, ya gargadi al’ummar kasar su kaucewa musabaha da kuma hada jiki a tsakanin su, domin kaucewa kamuwa da cutar Ebola, wanda yanzu haka ke cigaba da yaduwa a kasar.Yayin jawabi ga al’ummar kasar, shugaban yace an umurci ma’aikatar lafiya da ta bi diddigin duk wadanda suka gamu da wadanda suka kamu da cutar, wanda yanzu haka ta hallaka mutane 14.  

Shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni
Shugaban kasar Uganda, Yoweri Museveni
Talla

Ya zuwa yanzu an killace wasu likitoci bakwai da masu taimaka musu 13, saboda mu’amala da masu fama da cutar.

A cewar Museveni, daya daga cikin mutanen da su ka kamu da cutar ya mutu a wani asibiti da ke Yammacin babban birnin Uganda, Kampala.

Ya kara kashedin cewa, idan wani ya mutu da alamun cutar ya kada mutane su ce za su binne shi, maimakon haka, a kira ma’aikatan lafiya domin sun su ka fi sannin yadda za su tafiyar da lamarin.

Bullowar cutar a kwana kwana nan ya fara ne daga yankin Kibale, kusan kilomita 200 daga birnin Kampala inda wata ma’aikaciya da ta gudanar da ayyuka a asibitin Kagadi ta kamu da cutar.

Mai Magana da yawun Hukumar Lafiya ta Duniya, Tarik Jasarevic ya tabbatar da mutuwar mutum daya amma ya tabbatar da cewa babu sabuwar kamuwa daga cutar.

“Ina kira gareku, da ku kawo rahoton duk wata cuta da ta yi kama da Ebola, alamomin ta sun hada da zazzabi mai tsanani, amai,wasu lokuta da gudawa da kuma zubar jini” Museveni ya ce.

Kamuwa da cutar da kuma lokacin da za ta mamaye jikin mutum duka akalla a kwanaki 21 na farko.

Ana kuma iya yada wannan cuta ta hanyar musayar jini, ko kuma wani nau’in ruwa na jikin wanda ya kamu da cutar.

Daya daga cikin hadarin cutar shine ko likitoci da kan gwada mutum na dauke da ita kan iya kamuwa a lokacin da su ke gudanar da gwajin.

An sama cutar lakabin cutar Ebola daga wani rafi da ke kasar ta Congo, ana kuma samun ta ne daga namun daji wadanda su ka kamu da cutar irinsu birrai, Jemage, da Gada ko suna mace ko a raye.
 

Cutar ta kashe mutane 37 a shekarar 2007 haka kuma ta kashe mutane 170 a Arewacin kasar ta Congo.
 

Masana da dama sun fitar da magunguna wadanda har yanzu basu yi tasiri ba.

Hanya mafi saukin kare cutar kamar yadda hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana shi ne da mutum ya mutu a yi maza a binne shi ba tare da bata lokaci ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.