Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Shugaban mabiya Anglika ya nemi a kawo karshen rikicin Sudan ta Kudu

Shugaban Darikar Anglika na Duniya da ya kai ziyara a yankin da ake fama da tashin hankali a kasar Sudan ta Kudu, ya nemi a kawo karshen fadace fadacen.Justin Welby ya bukaci al’ummar kasra Sudan ta kudu mai fama da tashin hankali da kuma kasa ce ta mabiya Kiristanci da su kai zuciya nesa, kuma su tuna da wahalhalun da suka fuskanta a baya.Dubban mutane aka kashe a tashin hankalin daya barke tsakanin bangarori biyu masu fada da juna watau bangaren shugaba Salva Kiir da na tsohon mataimakinsa Riek Machar, tun lokacin da aka yi yunkurin kifar da gwamnatin sghugaba Kiir a cikin watan Disamba.Daga cikin abubuwan da Jagoran na mabiya Darikar Anglika ya maida hankali yayin wannan ziyarar da ya kai a Sudan ta kudu, akwai batun masu auren jinsi daya da Turawan yammacin Duniya ke hararan shugabannin Nahiyar Afruka akai.Batun Auren jinsi daya dai ya kasa samun karbuwa daga akasarin shugabannin Afruka da suka hada da Najeriya wadda ta rattaba Hannu kan dokar hana Auren Jinsi daya, sai Uganda inda shugaba Yuwere Mesovene ya ki amincewa da dokar hana auren na jinsi daya, amma ya ayyana masu luwadi da madigo a matsayin wadadan ked a wata damuwa. 

Shugaban mabiya darikar Anglika, Justin Welby.
Shugaban mabiya darikar Anglika, Justin Welby. REUTERS/Dylan Martinez
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.