Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Fada na ci gaba da zafafa a Sudan ta Kudu

Dubban dubatar Mutane na ci gaba da sulalewa daga Garuruwansu a kasar Sudan ta Kudu, sakamakon fadan da ake ci gaba da tafkawa a tsakanin Sojin Gwamnati, da ‘yan tawaye masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar, Riek Machar. Yanzu haka dai an bayyana yanda ‘yan gudun Hijirar ke ci gaba da Rayuwa a wasu wuraren da babu tabbas kan kula da Lafiyarsu.An bayyana cewa wannan ce babbar Jarrabawar da jaririyar kasar ke fuskanta, kuma babban Jami’in kula da bada agajin gaggawa na Majalisar dunkin Diniya a kasar ta Sudan ta Kudu Toby Lanzer, ya bayyana cewar basu da tabbas kan halinda ‘yan gudun hijirar da ke a wuraren da keda tashin Hankali suke ciki.Yace sun samu fiye da mutane Dubu 200 da suka dai dai ce a cikin wa’adin Makonni 2, kuma da alama adadin zai nunka wadannan alkaluman.Ya kara da cewa ko a Sansanin Majalisar dunkin Duniuya sun tabbatar da kona Gawawwakin mutane 70, tun bayan da tashin Hankalin ya barke.Babban Birnin kasar ta Sudan ta Kudu dai na da Garuruwa 3, da suka hada da Juba mai Tituna da Kura, kuma a halin yanzu jama’a sun watse daga birnin, kuma yanzu baa bin da ake ji sai karar tashin bindigogi cikin dare.An dai fara tashin Hankalin ne a ran 15 ga Watan Disamba tsakanin Sojoji masu goyon bayan Gwamnatin shugaban kasa Salva Kiir da kuma ‘yan Bindiga masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasra Riek Machar.Rikicin hakama ya ci gaba da ruruwa a sauran sassan kasar. 

Wasu mutanen da yakin sudan ta Kudu ya raba su da gidajen su
Wasu mutanen da yakin sudan ta Kudu ya raba su da gidajen su Reuters/Stringer
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.