Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

An cimma yarjejeniya kan rikicin Sudan Ta Kudu

Bangarori masu hamayya da juna a rikicin Sudan ta Kudu sun sanya hannu kan yarjejeniyar sulhu a tsakaninsu. Wannan na zuwa ne bayan share kusan makwanni uku suna tattaunawa a birnin Adis Ababa na kasar Habasha, a karkashin inuwar kungiyar kasashen yankin gabashin Afirka wato IGAD.A karkashin wannan yarjejeniya, bangaren shugaba Salva Kiir da kuma na tsohon mataimakinsa Riek Machar sun amince da tsagaita wuta a cikin sa’oi 24 daga lokacin da aka sanya hannu kan yarjejeniyar.To sai dai a cikin yarjejeniyar, babu batun sakin fursunonin siyasa da ke tsare a hannun gwamnatin Juba, wanda a can baya yake daya daga cikin muhimman sharuddan da Riek Machar ya shata kafin ajiye makamai. To sai dai yanzu haka wasu majiyoyi na cewa zai kasance abu mai wuya ga jagoran ‘yan tawayen ya iya tilastawa janar-janar da suka balle daga rundunar sojan kasar su ajiye makamansu, yayin da gwamnati ke ci gaba da rike wasu na hannun damarsu da yawansu aka ce ya kai 11.To sai dai za a ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu domin cimma matsaya kan sauran batutuwan da ba a kai ga warwarewa ba.An dai share tsawon makwanni 3 ana tattaunawa a tsakanin bangarorin biyu a birnin Adis Ababa na Habasha kafin cimma wannan matsaya. 

Wasu dakarun SPLA a  Sudan ta Kudu.
Wasu dakarun SPLA a Sudan ta Kudu. Reuters/George Philipas
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.