Isa ga babban shafi
Ghana-Cote D'ivoire

An cafke jagoran matasa magoya bayan Gbagbo a Ghana

Charles Ble Goude babban magoyi bayan tsohon shugaban kasar Cote’ d’Ivoire Laurent Gbagbo, da ke gudun hijira kimanin shekara daya da rabi, wanda kuma kotun kasar ta CI ta ba da sammacin kamawa, a jiya alhamis ya fada hannun jami’an tsaron kasar Ghana.

Tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo
Tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo REUTERS/Peter Dejong
Talla

Sai dai kuma har yanzu babu wani karin haske dangane da dalilan da suka sa mahukunta na Ghana kama shi.

Kasar Ghana dai makwabciya ce ta kusa ga kasar ta Cote d’Ivoire, kuma sau da dama wasu mahara da ake cewa magoya bayan Laurent Bagbo n da ke zaune a kasar Ghana na kai hare-hare a kan jami’an tsaron Cote d’Ivoire.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.