Isa ga babban shafi
Cote d’ivoire

Laurent Gbagbo na neman hadin kan ‘yan kasar Cote-D’Ivoire

Tsohon shugaban kasar Cote-D’Ivoire Laurent Gbagbo ya nemi sasanta kan ‘yan kasar, yayin da ya gana da Desmond Tutu.Tutu, da sauran dattawa da suka hada da Koffi Annan tsohon babban magatakarda na majalasar Dumkin Duniya, Mary Robinson tsohuwar shugaban kasar Ireland, sun kai ziyara ga Gbagbo a garin Korhogo na arewacin kasar inda ake tsare da shi.Dattawan bayan gana ta mintoci 15, sun nuna farin ciki su da yadda Gbagbo ya ke rungumar hanyoyin sasantawa. 

Shugaban kasar Côte d'Ivoire Alassane Ouattara da tsohon Praministan kasar Charles Konan Banny
Shugaban kasar Côte d'Ivoire Alassane Ouattara da tsohon Praministan kasar Charles Konan Banny Reuters/Thierry Gouegnon
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.