Isa ga babban shafi
Najeriya-Amurka

Goodluck ya nemi taimakon Amurka don magance matsalar tsaro a Najeriya

Shugaban Najeriya goodluck Jonathan ya nemi taimakon Amurka wajen yaki da Boko Haram bayan ya gana da Janar Carter Ham babban hafsan Sojan Amurka da ke kula da Nahiyar Afrika. Wannan kuma na zuwa ne bayan Kwamandan ya yi gargadin hadin kan mayaka a kasashen Afrika barazana ce ga Amurka da kasashen Turai.

Sakatariyar Harakokin Wajen Amurka Hillary Clinton tare da Goodluck Jonathan a ziyarar da ta kai a Najeriya
Sakatariyar Harakokin Wajen Amurka Hillary Clinton tare da Goodluck Jonathan a ziyarar da ta kai a Najeriya REUTERS/Jacquelyn Martin/Pool
Talla

Tun kafin ya gana da Jonathan Mista Ham ya bayyana cewa akwai alaka tsakanin Boko Haram da kungiyar Al Qaeda da ke yankin Arewacin Afrika.

Wata sanarwa daga Fadar Shugaban Najeriya an bayyana cewar batutuwan da Jonathan ya tattauna da Ham sun kunshi batun magance matsalar Boko Haram inda kuma shugaban ya nemi taimakon Amurka don magance matsalar.

Sanarwar ta kara da cewa Jonathan ya shaidawa Janar Ham ziyarar shi zuwa kasar Mali a watan Oktoba tare da bayyana yukurin da kasashen Kungiyar ECOWAS ke yi don magance rikicin kasar.

Tuni dai kasashen Jami’an diflomasiyar Amurka suka ce ‘yayan kungiyar Boko Haram suna samun horo a Arewacin Mali da ke karkashin ikon Kungiyar Ansar Dine.

A kwanan baya ne kuma Gwamnatin Amurka ta saka sunayen wasu Shugabannin Boko Haram guda Uku a cikin jerin sunayen ‘Yan ta’adda ba tare da saka sunan kungiyar ba.

Sai dai kuma an dade kungiyar Boko Haram na ikirarin cewar yakin da ta ke yi tana yi ne domin daukar fansar kisan gillar da Jami’an tsaron Najeriya suka yi wa shugabanninta da iyalan Mambobinta a zamanin mulkin Marigayi Yar’Adua.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.