Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan Sandan Najeriya sun ce sun sake cafke wasu ‘Yan bindigar da suka tsere

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da sake cafke mutane 25 daga cikin 30 da suka tsere a harin da wasu ‘Yan bindiga suka kai a Ofishin ‘Yan Sandan da ke Abuja, rundunar ‘Yan sandan tace ta yaba da rawar da jami’anta suka taka wajen gudanar da aikin ba tare da jikkata jama’a ba.

MD Abubakar  Sufeto Janar na 'Yan sandan Najeriya
MD Abubakar Sufeto Janar na 'Yan sandan Najeriya RFI Hausa
Talla

Kakakin Rundunar ‘Yan sandan Frank Mba yace ‘yan sandan sun yi amfani da basira wajen cafke ‘Yan bindigar tare da kaucewa jikkata fararen hula wajen farautarsu

A jiya Litinin ne dai ‘Yan bindiga suka kai hari a hedikwatar ‘Yan sanda a Abuja wanda hakan ya ba wadanda ake tsare da su kusan 30 tserewa daga ofishin ‘Yan sandan tare da kuma kashe ‘Yan sanda biyu.

Har yanzu dai babu wani tabbacin wadanda suka kai harin.

A Wani Rahoto da kungiyar Amnesty international ta fitar an bayyana kimanin mutane 100 ne ‘Yan sandan Najeirya suka cafke wadanda ake zargin suna da alaka da kungiyar Boko Haram.

A makon jiya nerundunar Sojin Najeriya ta bayyana kudirin bada kayutar kudi daga Miliyan Goma zuwa Naira Miliyan Hamsin ga duk wanda ya taimaka aka kama Shugabannin kungiyar Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.