Isa ga babban shafi
Koriya ta Kudu

Shugabar Koriya ta fuskanci fushin iyalan mutanen da suka nutse a teku

Shugaba kasar Koriya ta Kudu, Park Geun-Hye ta fuskanci fushin iyalan wadanda suka nutse a ruwan teku inda suka zargi hukumomin kasar da gazawa wajen ganin an gaggauta nemo wadanda hadarin ya rutsa da su.

Shugabar kasar Koriya ta Kudu
Shugabar kasar Koriya ta Kudu REUTERS/Yves Herman
Talla

A ranar litinin da ta gabata, jirgin ruwan dauke da fasinjoji sama da 400 ya nutse a kasar mafi aksarinsu dalibai.

Izuwa lokacin hada wannan rahoto, bayanai sun nuna cewa mutane 11 ne aka gano gawawwakinsu yayin da ake ci gaba da gudanar da neman mutanen.

“Me kike yi a lokacin da mutane suke mutuwa, lokaci na kurewa” Inji wata mata da ta datse Park a lokacin da take kokarin yin jawabi ga iyalan.

Sai dai mafi yawan fushin da iyalan suka nuna, yafi karewa ne akan shugaban rundunar tsaron gabar tekun ruwan kasar Kim Suk-Kyoon, inda iyalan suka nuna gazawarsa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.