Isa ga babban shafi
Korea

Dangi da yakin Korea ya raba zasu yi Zumunci

A karon farko tun shekarar 2010 kasashen Korea ta Arewa da Korea ta Kudu sun amince da yarjejeniyar ba dangi da yaki ya raba damar gudanar da zumunci a tsakaninsu a cikin watan Fabrairu. Miliyoyan mutanen Korea ne Yaki ya raba su da danginsu bayan warewar Korea ta kudu da Arewa.

Wata Tsohuwa a kasar korea ta Kudu mai suna Wang So-Goon tana kuka a lokacin da take ganawa da danginta da ke zama a Korea ta Arewa
Wata Tsohuwa a kasar korea ta Kudu mai suna Wang So-Goon tana kuka a lokacin da take ganawa da danginta da ke zama a Korea ta Arewa AFP/Korea Pool
Talla

Kasashen biyu da ke yi wa juna barazanar yaki sun amince ‘yan uwa su gudanar da zumunci da danginsu da suka rabu tsakanin ranakun 20 zuwa 25 na watan Fabrairu.

Sai dai masu lura da rikicin kasashen biyu suna ganin babu tabbas ko ‘Yan uwa zasu samu damar haduwa da ‘Yan uwansu saboda tankiyar da ke tsakanin kasashen biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.