Isa ga babban shafi
Korea ta Kudu

Atisayen hadin gwiwar sojojin Amurka da na Koriya ta Kudu

An kaddamar da atisayen hadin gwiwa na shekara shekara tsakanin sojojin Amurka da takwarorinsu na kasar Korea ta Kudu a daidai lokacin da Korea ta Arewa ke nuna adawarta da wannan atisaye.

Talla

Atisayen na wannan karo wanda sojojin Amurka 12,700 ke taka rawa a cikinsa, na zuwa ne a daidai lokacin da iyalai daga kasashen biyu ke ganawa da junansu bayan share tsawon shekaru ba tare da sun samu irin wannan damar ba.

Amurka dai na da kyakkyawar alaka ta tsaro da kasar Koriya ta Kudu, alakar da Koriya ta Arewa ke kallo a matsayin barazana a gare ta. Shekaru biyu da suka gabata, Koriya ta Arewa ta yi gwaji wasu makaman nukiliya masu cin dogon zango, a matsayin martani dangane da wannan atisaye da kasashen biyu ke yi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.