Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire-Najeriya

Ebola: An yi wankan Gishiri a Cote d’Ivoire

Kasar Cote d’Ivoire ta samu kanta cikin yanayi irin na Najeriya inda aka dinga umurtan mutane su sha ruwan Gishiri ko su tauna Albasa don kaucewa kamuwa da cutar Ebola da ke ci gaba da kisa a yammacin Afrika.

Wasu 'Yan Najeriya suna jika gishiri a cikin bokitin wanka domin kariya ga cutar Ebola
Wasu 'Yan Najeriya suna jika gishiri a cikin bokitin wanka domin kariya ga cutar Ebola nairaland
Talla

Rahotanni sun ce tun a karshen makon da ya gabata ne ake ta yada labarin isar cutar Ebola a kasar ta wayar salula, tare da umurtar ‘yan kasar su jika gishiri su sha, ko su tauna albasa.

Wani dan kasuwa Evariste Kouassi a kauyen Kotouba ya ce mutane da dama sun bi umurnin ba tare da samun umurnin likita ba.

Zuwa yanzu dai ba a samu rahoton bullar cutar Ebola ba a kasar Cote d’Ivoire bayan ta yi sanadin mutuwar mutane kimanin 1,500 a kasashen Guinea da Liberia da Saliyo da Najeriy.

Irin wannan jita-jitar ce aka yada a Najeriya ta umurtan mutane yi amfani da ruwan gishiri domin samun kariya daga kamuwa da cutar Ebola.

Mutanen Najeriya da dama ne suka yi wanka da ruwan gishiri bayan da wani mutumin Liberia ya shigo da cutar a garin Lagos.

Mutane 5 suka mutu a Najeriya, yayin da kuma Mahukuntan kasar suka ce yanzu mutum guda ne ya rage cikin mutanen da aka killace da suka yi mu’amula da mutumin Liberia, bayan sallamar wasu daga cikinsu.

Domin dakile bazuwar Ebola, Gwamnatin Najeriya ta sanar da rufe daukacin makarantun Firamare da Sakandaren kasar. Ministan ilimi Ibrahim Shekarau yace dokar hana bude makarantu ta shafi makarantun gwamnati da masu zaman kansu har zuwa 13 ga watan Oktoba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.