Isa ga babban shafi
Ebola

Likitocin Amurka da suka kamu da Ebola sun warke

Asibitin Jami’ar Emory a Atlanta kasar Amurka ta sallami Likitocin da suka kamu da Cutar Ebola a Liberia, Kent Brantly da Nancy Writebol, bayan an yi amfani da maganin gwajin cutar da aka samar wanda kuma ya warkar da su. Kwararru kan sha’anin kiwon lafiya, sun nuna damuwarsu dangane da yadda ake aiwatar da siyasar raba maganin na Ebola da aka samu.

Likitan Amurka Kent Branly, wanda ya warke daga cutar Ebola bayan ya kamu da cutar a Liberia
Likitan Amurka Kent Branly, wanda ya warke daga cutar Ebola bayan ya kamu da cutar a Liberia REUTERS/Samaritan's Purse/Handout via Reuters
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin kiwon lafiya a Amurka suka tabbatar da cewa wasu ‘yan kasar biyu da suka kamu da cutar a lokacin da suke aiki a Liberia sun warke daga cutar.

Dakta Ezekiel Emmanuel na jami’ar Pennsylvania da kuma Annette Rid ta Kings College da ke birnin London, sun bayyana a cikin mujallar kiwon lafiya ta The Lancet Medical Journal cewa akwai bukatar nuna adalci a game da yadda ake raba maganin yaki da cutar da yanzu haka kwararru suka samar a kasar Amurka.

Masu binciken sun bayyana cewa a halin yanzu ana raba maganin yaki da cutar ne mai suna Zmapp ga jami’an kiwon lafiya kawai, a daidai lokacin da kasashe ke ci gaba da fama da wannan cuta da ke daukar rayukan jama’a kusan a kowace rana ta Allah.

Yanzu haka dai kasashen da suka mallaki maganin warkar da cutar kamar Amurka da kuma Canada, sun ce maganin ya yi karancin da ba za a iya bayar da shi a wadace ga kasashen yammacin Afirka da ke fama da cutar Ebola ba.

Sai dai wasu masana a fannin kiwon lafiya, na ganin cewa ta la’akari da yadda ake fama da karancin maganin na Zmapp, ya dace a ci gaba da raba shi ga jami’an kiwon lafiya kawai, domin kuwa su ne rukunin jama’ar da suka fi kasancewa a cikin hatsari wajen mu’amala da masu dauke cutar ta Ebola.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.