Isa ga babban shafi
Najeriya

Janar Muhammadu Buhari ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takara

Tsohon Shugaban Najeriya Janar Muhammadu Buhari ya shaidawa magoya bayansa cewar zai tsaya takarar shugabancin kasar a shekara mai zuwa idan Jam’iyarsa tsaidashi a zaben shekarar 2015 da ke zuwa

Janar Muhammadu Buhari dan takarar CPC a zaben shugaban kasar Najeriya 2011
Janar Muhammadu Buhari dan takarar CPC a zaben shugaban kasar Najeriya 2011 RFI Hausa
Talla

Yayin da yake jawabi ga kungiyoyin magoya bayan sa a babban birnin tarayya na Abuja, Buhari ya bayyana kalubalen da ke gaban Najeriya yau a matsayin mai girma, inda yace matakin farko da ke gabansu shine raba wadanda suka kasa gudanar da mulki da mulkin kasar.

Tsohon shugaban kasar ya zargi Jam’iyar PDP da kasa samarwa kasar ci gaba a cikin shekaru 15 da suka gabata, inda ya roki magoya bayansa da su goyawa duk wanda Jam’iyar su ta APC ta tsayar.

Matsalar tsaro a tarayyar Najeriyar dai na cikin ababen da a halin yanzu ake kallo a matsayin kasawar gwamnatin jam’iyyar PDP da kuma ke kwadayen dorewa da mulki bayan da Jam’iyyar ta baiwa shugaba Jonathan tiketin tsayawa takara babu hamayya.

Sai dai a wannan karon kam da wuya Jonathan ya samu karbuwa daga al’ummar Arewacin kasar musamman lura da yanda ya yi bayyanawa a baya cewar baya da niyyar zarcewa kan mulki, amma daga bisani ya zo ya canja ra’ayi.

Zargin cinikin makamai da ake yiwa shugaban kungiyar Kiristocin Najeriyar Ayo Oritsejafor da aka kama Jirginsa a kasar Afruka ta kudu ma, na daga cikin ababen da suka janyowa shugaba Jonathan bakin jini ga ‘yan Arewa, lura da yanda ya yi kane-kane ga kin bari a yi binciken wadanda ake zargi.

Baya ga wannan kuma akwai batun alakarsa da tsohon gwamnan jihar Borno Ali Modu Sherif wanda binciken wani Baturen kasar Australiya ya zarga da Hannu ga tallafawa ‘yan Boko Haram, da kuma gaggawar wanke tsohon babban Hafsan Sojin kasar chief Azubuike Ihejirika daga zargin da ake masa tare da Ali Modu Sherif.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.