Cuba ta aike da likitoci Tsibiri Martinique na kasar Faransa
Kasar Cuba ta aike da kwararrun likitoci 15 da suka sauka tsibirin Martinique dake karkashin ikon Faransa don taimakawa wajen yaki da annobar Covid 19 a wannan yanki na kasar.
Wallafawa ranar:
Jami’an kiwon lafiyar sun sauka ne daga cikin jirgin dake dauke da su,fuskoki a rufe,dauke da tutar kasar ta Cuba,za su kuma share watanni uku don ganin sun taka gaggarumar rawa a wannan yaki da cutar covid 19 da kuma tallafawa wajen karawa jami’an kiwon lafiyar tsibirin na Martinique sani a wasu fanoni daban da kuma suka jibanci kiwon lafiya.
A haka Faransa ta kasance kasa ta uku da za ta amfana da tallafin kasar Cuba ta bangaren kiwon lafiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu