Dan Najeriya ya shiga jerin manyan 'yan wasan Tennis 20 na Duniya
Wani rahoto da hukumar shirya gasar Tennis ta Duniya ITTF ta fitar a jiya ya nuna cewa Quadri Aruna ya shiga jerin manyan ‘Yan wasan Tennis 20 na duniya.
Wallafawa ranar:
A cikin jadawalin da hukumar ta fitar, dan Najeriyar ya samu matsayi na 19.
A jadawali 2 na baya-bayan nan da hukumar ta fitar, Aruna na matsayi na 22 bayan da ya yi rashin nasara a gasar cin kofin Tennis ta duniya wadda ta gudana a kasar Koriya.
Yayin da zakaran gasar a Nahiyar Africa Dan Kasar Masar Omar Assar, shima ya samu matsawa gaba zuwa matsayi na 16 a Duniya.
Kazalika Aruna, na ci gaba da mamayar gasar ITTF ta 2024 wadda aka fara daga ranar Litinin 15 ga watan Afrilu, inda ya lallasa Daniel Gonzalez da ci 11 da 6, 11 da 4, 11 da 6, da kuma 11 da 6.
A yau Laraba ne ake sa ran Aruna zai buga wasa da Dan kasar Portugal Marcos Freitas, a filin wasa na Galaxy Arena.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu