Isa ga babban shafi

Rafael Nadal ya yi nasara a gasar Barcelona Open bayan dawowarsa daga jinya

Zakaran Kwallon Tennis na duniya Rafael Nadal, ya yi nasara a gasar Barcelona Open, bayan dawowarsa daga doguwar jinyar da ya yi fama da ita.

Rafael Nadal après sa défaite contre l'Australien Jordan Thompson au tournoi de Brisbane, le 5 janvier 2024.
Rafael Nadal après sa défaite contre l'Australien Jordan Thompson au tournoi de Brisbane, le 5 janvier 2024. © AFP / PATRICK HAMILTON
Talla

Dan kasar Spain mai shekaru 38 kuma zakaran gasar Grand slams har sau 22, ya yi nasara akan abokin karawarsa Flavio Cobolli dan kasar Italiya da ci 6-2 6-3 a zagayen farko na wasan.

Wasan na ranar Talata da Nadal ya buga, shi ne karon farko tun watan Janairu sakamakon raunin da ya samu a kunkuminsa da kuma matsala a cikinsa.

Foto de archivo de Rafael Nadal
Foto de archivo de Rafael Nadal AP - Hamish Blair

Ana hasashen dai shekarar 2024 da muke ciki ta zama ta karshe da Nadal din zai buga wasanni kafin ya ajiye takalmansa.

A gasar French Open ta shekarar da ta gabata ne ya samu rauni a kunkuminsa, inda tun a lokacin ya ke bayyana cewa ya shirya ajiye Takalmansa a karshen kakar nan.

A baya dai Nadal ya lashe gasar French Open sau 14, da Barcelona Open sau 12, sai Grand Slam sau 22 da sauran su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.