Isa ga babban shafi

Real Madrid ta raba maki da Rayo Vallecano a gasar La Ligar Spain

Real Madrid, wadda ke kan gaba a gasar La Ligar Spain ta buga canjaras a wasan da ta yi da buga da Rayo Vallecano a Lahadi, lamarin da ke bai wa Girona da Barcelona kwarin gwiwa a fafutukar lashe kofin na La Ligar.

Wasu 'yan wasan Real Madrid.
Wasu 'yan wasan Real Madrid. AP - Jose Breton
Talla

Madrid ce ta fara saka kwallo a wasan, ta hannun Joselu, wanda ya yi amfani da kwallon da Fede Valverde ya ba shi, amma Rayo Vallecano ta mayar da martani ta bugun daga- ka- sai -mai tsaron raga, sakamakon hannu da Eduardo Camavinga ya saka wa kwallo, kuma Raul de Tomas ya buga,

Real Madrid ba ta samar da damammakin saka kwallo a raga masu armashi ba, kuma haka aka tashi wasan ba kare-bin -damo, wato kujnen doki 1-1.

Sai dai duk da wannan canjaras din, Real Madrid, wadda sau 35 ta lashe kofin La Ligar Spain tana kan gaba a teburin gasar da tazarar maki 6 tsakaninta da Girona, wadda ke matsayi na 2, kuma za ta ziyarci Athletic Bilbao a wannan Litinin.

Tazarar maki 8 ne tsakanin Real Madrid da abokiyar  hamayyarta, Barcelona wadda ke matsayi na 3, kuma da kyar ta doke Celta Vigo a ranar Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.