Isa ga babban shafi

Man United ta karfafa damar kasancewa a sahun kungiyoyi 4 na farko a Firimiya

Manchester United ta samu nasarar doke Luton har gida da ci 2 da 1 a jiya Lahadi, lamarin da ya ba ta kwarin gwiwar sa ran kammalawa a cikin kungiyoyi hudu na farko-farko a gasar Firimiyar Ingila. 

'Yan wasan Manchester United a yayin murnar kwallon da  r Rasmus Hojlund ya ci.
'Yan wasan Manchester United a yayin murnar kwallon da r Rasmus Hojlund ya ci. REUTERS - CARL RECINE
Talla

Kwallaye biyu da dan wasan gaba na kasar Denmark, Rasmus Hojlund ne suka bai wa United wannan nasara mai matukar mahimmanci a gidan Luton. 

Dan wasan gaban na Denmark, wanda ya ke kan ganiyarsa a halin yanzu, ya yi amfani da damar da kurakuran masu tsaron bayan Luton ya samar ne ya saka kwallo a daidai dakika ta 37, kana ya ci kwallo ta biyu bayan mitina 7 da samuwar ta farkon. 

Kungiyar Luton, wadda ke cikin hatsarin rikitowa daga Firmiyar Ingila ta mayar da martini mai armashi, inda a cikin minti na 14 da wasa Carlton Morris ya saka wa wata kwallo kai, ta fada ragar United. 

United, wadda ke matsayi na 6 a teburin gasar Firmiyar Ingila ta yi ta baras da damammakin saka kwallo a raga bayan da aka dawo hutun rabin lokaci, a yayin da a dakikokin karshe na wasan, kiris ya rage dan wasan Luton Ross Barkley ya jefa kwallo a ragar United. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.