Isa ga babban shafi

Super Eagles ta shiryawa haduwa da Bafana Bafana ta Afrika ta kudu

Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta isa birnin Bouke na Ivory Coast don fara atisayen tunkarar haduwarta da Bafana Bafana ta Afrika ta kudu a wasan gab da na karshe da manyan tawagogin biyu za su kara da juna don fitar da wadda za ta haska a wasan karshe na cin kofin AFCON

Tawagar Super Eagles ta Najeriya da ke fafatawa a gasar AFCON.
Tawagar Super Eagles ta Najeriya da ke fafatawa a gasar AFCON. © AFCON 2023
Talla

Super Eagles wadda kwallo guda aka iya zura mata, ta samu kai wa wannan matakin ne bayan fitar da Angola da kwallo 1 mai ban haushi, Sai dai  Afrika ta kudu ta doka wasanni 4 a jere karkashin gasar ba tare da anyi nasara akanta ba, nasarar da ake alakantawa da kwazon mai tsaron ragar kasar Ronwen Williams wanda ya nuna matukar bajinta yayin bugun fenariti tsakaninsu da Cape Verde.

A bangare guda Super Eagles tun bayan lashe kofin makamanciyar gasar fiye da shekaru 10 da suka gabata, ta yi nasarar isa irin wannan mataki sau 5 amma duka bata iya kara gaba daga wannan mataki ba in banda sau 1 tal, yayinda Afrika ta kudu wadda rabonta da lashe kofin gasar tun 1996 lokaci na karshe da ta kai irin wannan mataki shi ne a shekarar 2000.

Duk da karfi da darajar tawagar ta Super Eagles ta fuskar manyan ‘yan wasan da ke kunshe cikinta, masana sun bayyana haduwar ta gobe a matsayin wadda ba za ta zo mata da sauki ba ko kadan.

OSIMHEN

Babu dai tabbacin Najeriya ta doka wasan tare da Victor Osimhen wanda aka fitar daga fili a karawarsu da Angola saboda ciwon ciki, lura da cewa tawagar ta bar shi a Abidjan yayin bulaguronsu na jiya zuwa Bouake wanda har sai likita ya tabbatar da lafiyarsa ne zai iya bin tawagar kowanne lokaci a yau Talata, sabanin haka kai tsaye zai iya rasa karawar wadda kuma babban kalubale ne ga Super Eagles.

Duk da cewa Osimhen bai zura kwallaye kamar yadda ka yi hasashe ba, amma y ana taimakawa tawagar yayinda hankulan masu tsaron bayan kasashe ke karkata kanshi.

A bangare guda, Zubin ‘yan wasan da Hugo Broos ya yiwa tawagar ta Bafana-Bafana ya tattara ‘yan wasan Sundowns gabaki daya a matsayin masu tsaron baya, batun da masana ke cewa lallai za su iya baiwa Super Eagles matsala.

Haduwa ta karshe tsakanin Super Eagles da Bafana-Bafana a 2019 shi ne nasarar da Najeriya ta yi da kwallo 1 mai ban haushi kwallon da Kyaftin William Troost-Ekong ya zura a minti na 89 gab da tashi daga wasa.

Tarihin haduwar bangarorin biyu ya nuna yadda Najeriya ta yi nasara a haduwa 7 Afrika ta kudu a guda 2 yayinda suka yi canjaras a 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.