Isa ga babban shafi

Hukumar kwallon kafar Kamaru ta ki amincewa da murabus din Eto’o

Hukumar kwallon kafar kasar Kamaru, ta ki amincewa da bukatar ajiye aiki da tsohon dan wasan gaba na kasar, Samuel Eto’o, ya gabatar mata.

Tsohon dan wasan gaban Kamaru, kuma shugaban hukumar kwallon kafar kasar, Samuel Eto kenan
Tsohon dan wasan gaban Kamaru, kuma shugaban hukumar kwallon kafar kasar, Samuel Eto kenan AFP - BERTRAND GUAY
Talla

A ranar Litinin ne, Eto’o ya mika takardar ajiye mukamin shugabancin hukumar, yayin wani taron ganawa da aka gudanar a birnin Yaounde.

Tsohon dan wasan na Kamaru y ace matakin nasa ya biyo bayan gazawar ‘yan wasan kasar na kasa tabukawa a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON da ke gudana a kasar Ivory Coast.

Sai dai mambobin hukumar sun ce suna da kwarin gwiwa a kansa na ci gaba da aiwatar da sauye-sauye da kuma samar da ci gaba ga bangaren kwallon kafar kasar a kowanne mataki.

Dan wasan wanda ya taba lashe gwarzon dan kwallon Afirka har sau hudu, ya samu cikakken goyon baya daga bangarori da dama, duk da cewa ya fuskanci suka game da yadda yake tafiyar da shugabancin hukumar da kuma zargin rashawa a shekarar bara.

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai CAF, yanzu haka tana gudanar da bincike kan abin da ta kira zarge-zarge masu tsauri daga manyan masu ruwa da tsaki na kasar Kamaru da suke yiwa Samuel Eto’o.

Hukumar ta lura da cewa, tsohon dan wasan na Barcelona da kuma Inter Milan, har yanzu babu wani laifi da aka same shi da shi, sai dai nan gaba idan an kammala bincike.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.