Isa ga babban shafi

Mo Salah ya bukaci kawo karshen kisan Falasdinawa a Gaza

Dan wasan Masar da Liverpool Mohamed Salah ya yi kira da a kawo karshen kisan kiyashi da ake yi a Gaza, yana mai cewa dole ne kuma a shigar da kayan agajin jin kai cikin gaggawa a yankin Falasdinawa da aka yi wa kawanya.

Dan wasan Masar da Liverpool Mohamed Salah
Dan wasan Masar da Liverpool Mohamed Salah AFP
Talla

Dan wasan mai shekaru 31 da haifuwa ya yi tsokaci na farko kan rikicin Isra'ila da Gaza a ranar Laraba a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna bacin rai game da mutuwar kusan mutane 500 a wani fashewa da aka yi a asibitin Larabawa na al-Ahli da ke birnin Gaza.

Hari kan asibitin Gaza

Hukumomin Falasdinawa sun ce harin da Isra'ila ta kai ta sama ne ya haddasa fashewar, yayin da Isra'ila ta ce fashewar ta faru ne sakamakon wani makamin roka da kungiyar Hamas ta Palasdinawa ta harba, zargin da tuni da dama suka musanta.

“Babu sauƙin yin magana a irin wannan yanayi, saboda lamarin ya wuce gona da iri da rashin tausayi” In ji Salah a wani faifan bidiyo da mabiyansa miliyan 62.7 suka kalla a Instagram.

Shan suka

An caccaki dan wasan wanda shi ne kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Masar, da rashin yin magana domin kare Falasdinawa, kuma wasu masu suka sun fara wani gangamin ta yanar gizo don janyewa daga shafukan s ana sada zumunta.

Dan wasan da ya lashe gasar zakarun Turai da Premier tare da Liverpool, Salah na daya daga cikin fitattun 'yan wasa a kasashen Larabawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.