Isa ga babban shafi

Al-Ittihad ta mika tayin fam miliyan 118 ga Salah na Liverpool

Wata tawagar jami’an kungiyar kwallon kafa ta Al-Ittihad a Saudiya ta yi tattaki zuwa Ingila don tattaunawa da Mohamed Salah na Liverpool kan shirin komawarsa lig din Saudiya da taka leda.

Mohamed Salah na Masar da ke take leda da Liverpool mai doka gasar Firimiyar Ingila.
Mohamed Salah na Masar da ke take leda da Liverpool mai doka gasar Firimiyar Ingila. Action Images via Reuters - LEE SMITH
Talla

Wannan batu dai na tabbatar da jita-jitar da ke alakanta tauraron na Liverpool da bin sahun takwarorinsa irinsu Jordan Henderson da Roberto Firmino da kuma Fabinho wajen kulla kwantiragi da Saudiyan.

Jaridar Mail Sport ta bayyana cewa Al-Ittihad ta mika tayin fam miliyan 118 ga Salah dan Masar kuma akwai tabbacin ya amince da tayin duk da yadda kungiyar ke ci gaba da nanata cewa dan wasan ba na sayarwa ba ne.

Liverpool dai na ci gaba kaucewa duk wata tattaunawa da ta shafi sayar da Salah, lura da cewa rabuwa da shi za ta haddasa mata gagarumar matsala.

A bangare guda idan har Liverpool ta amince da sayar da Salah kai tsaye hakan zai shafi shirin Jurgen Klopp a Anfield wanda kacokan ya dora buri kan dan wasan.

Wasu majiyoyi na cewa manajan na Liverpool ya fusata matuka da yadda kungiyar ta tarbi tawagar ta Saudiya don tattaunawa kan Salah.

Kasar ta yankin Gulf dai na kallon Salah a matsayin wata zinariya mallakinsu kasancewar sa dan wasa balarabe mafi daukaka a Duniya, wanda zai taimaka matuka wajen kara kima ga lig din na Saudiya gabanin kasar ta karbi bakoncin gasar cin kofin duniya ta kungiyoyi wato Club World Cup a watan Disamba mai zuwa.

Dillalin zakaran na Liverpool Ramy Abbas, ya tabbatar da cewa babu shirin tafiyar dan wasan a wannan kaka, sai dai bai karin bayani kan ko akwai shirin tafiyar ta saw ani lokaci a nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.