Isa ga babban shafi

FIFA ta dage dakatarwar da ta yi wa Zimbabwe na halartar gasar AFCON

Fifa ta dage dakatarwar da ta yi wa hukumar kwallon kafa ta Zimbabwe, sannan ta kafa wani kwamiti na wucin gadi da zai sanya idanu kan ayyukan hukumar har tsawon shekara guda.

Tawagar Zimbabwe kenan
Tawagar Zimbabwe kenan © goal
Talla

Matakin da hukumar kwallon kafa ta duniya ta dauka na nufin cewa a ranar Laraba ne kasar Zimbabwe za ta kasance cikin jerin sunayen kasashen da za su fafata a gasar cin kofin duniya na shekarar 2026.

Fifa ta dakatar da Zimbabwe a watan Fabrairun 2022 bayan da gwamnatin kasar ta nada hukumar wasanni ta daban tare da dakatar da Zifa, wato wadda FIFA ta saniu a hukumance.

Fifa ta haramta katsalandan da wasu gwamnatoci ke yi a harkar kwallon kafar kasashensu.

Hakan ta sanya aka dakatar da Zimbabwe shiga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2023, da kuma gasar ta AFCON ta mata da za a yi a 2024, da dai sauran mabanbantan gasa, ciki kuwa har da dakatar da tallafin da FIFA ke bawa hukumar kwallon kafar kasar ta Zifa.

Daga cikin zarge-zargen da hukumar FIFA ke yiwa gwamnatin kasar dai, akwai batun tsoma baki kan zargin cin zarafin da ake yiwa alkalan wasa mata, da kuma aikata zamba a tsakanin shugabannin hukumar da ake samu.

A watan Satumbar 2022, Fifa ta dakatar da Obert Zhoya tsohon jami'in Zifa na tsawon shekaru biyar bayan an same shi da laifin cin zarafin wasu alkalan wasa mata guda uku.

Sabon kwamitin da aka kafa na daidaita al'amuran ya kasance an ba shi umarnin kammala aikinsa kafin ranar 30 ga watan Yuni 2024. Zai sake fasalin Zifa, da kuma sake duba dokokin hukumar hadi da shirya zaben shugabannin da zza su jagoranci ita wannan hukuma.

Kwamitin zai kuma tabbatar da mika kudaden da ya dace ga sabuwar hukumar ta Zifa kuma an bukaci kwamitin ya cimma wata yarjejeniya ta musamman ta hadin gwiwa don magance matsalolin cin zarafi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.