Isa ga babban shafi

FIFA ta ware $152m saboda kofin duniya na Mata a 2023

Shugaban FIFA Gianni Infantino ya tabbatar zunzurutun kudi har dala miliyan 152 a matsayin kyautar da aka warewa gasar cin kofin duniya ta mata da Australia da New Zealand zasu karbi bakwanci.

'Yar wasan tawagar mata ta Sweden Kosovare Asllani na murnar zura kwallo ta farko, a Gasar cin kofin duniya na mata ta FIFA - UEFA - Rukunin A - Sweden da Jamhuriyar Ireland . 12/04/2022.
'Yar wasan tawagar mata ta Sweden Kosovare Asllani na murnar zura kwallo ta farko, a Gasar cin kofin duniya na mata ta FIFA - UEFA - Rukunin A - Sweden da Jamhuriyar Ireland . 12/04/2022. TT News Agency via REUTERS - TT NEWS AGENCY
Talla

Infantino ya tabbatar da hakan ne a lokacin da yake ganawa da shugabar Hukumar Kasuwanci ta duniya Dr Ngozi Okonjo-Iweala.

Gasar kofin duniya ta Mata

A ranar 20 ga watan Yuli ne za a fara gasar kwallon kafa mafi girma ta mata kuma Australia da New Zealand za su dauki nauyin shirya gasar, yayin da FIFA ke shirin kara yawan kudaden kyaututtukan da za’a samu fiye da yadda aka gani shekaru hudu baya wato a 2019.

Shugaban na FIFA yace a matsayisa na mahaifin kyawawan 'ya'ya mata hudu, ya kwana da sanin yadda Mata suke bukatar kulawa sosai.

Hakan ya sa zasu yi kokarin cimma burin samar da daidaito ta fannin biyan kudade a gasar cin kofin duniya na maza 26 da '27 na mata.

Daidaito

Jami’in yace gagarumin ci gaba ne wajen ware dala miliyan 152 a gasar farko ta kungiyoyi 32 na Mata daga $30m a ƙungiyoyi 24 a shekarar 2019, wanda ya ninsa sau 10 da yadda abin yake a 2015, duk da cewa yana kasa da kyautar $ 440m da aka kashe a gasar cin kofin duniya ta maza 32 da aka yi bara a kasar Qatar.

A gasar cin kofin duniya ta mata ta 2019, zakarun gasar sun samu dala miliyan 4 yayin da kowace kasar da ta shiga gasar ta samu $750,000.

Shugaban hukumar FIFA, cikin wata sanarwa da ya fitar ta shafin intanet na hukumar kwallon kafa ta duniya, ya ce tuni FIFA ta ba da misali da kara adadin kudaden da ake kashewa a gasar cin kofin duniya ta mata na shekarar 2023 zuwa dala miliyan 152, wanda ya ninka adadin da aka biya a shekarar 2019 kuma sau 10 fiye da na shekarar 2015 kafin zaben sa a matsayin shugaban FIFA.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.