Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Chelsea ta rike PSG a Paris

Chelsea da Paris Saint-Germain sun yi kunnen doki ne ci 1 da 1 a Paris a gasar zakarun Turai da suka fafata kafin nan gaba a fitar da gwani tsakanin kungiyoyin biyu a Stamford Bridge a karawa ta biyu a gidan Chelsea.

'Yan wasan PSG
'Yan wasan PSG Foto: RFI
Talla

A daya bangaren, Shakhtar Donetsk ta rike Bayern Munich ne babu ci a fafatawar da suka yi a Ukraine, kafin su sake haduwa Jamus.

Alkalin wasa ya kori Xavi Alonso da jan kati bayan an dawo hutun rabin lokaci, a yayin da dan wasan na Spain ke bikin haskawa karo na 100 a gasar zakarun Turai.

A yau Laraba ne FC Basel za ta karbi bakuncin FC Porto. Real Madrid kuma zata kai wa Schalke 04 ziyara ne a Jamus.

Kocin Schalke Roberto Di Matteo ya ce a wannan karon ba za su yadda Real Marid ta ba su kashi ba kamar bara inda ta yi waje da su da jimillar kwallaye 9-2.

Tsohon kocin na Chelsea ya ce yana fatar ‘yan wasan shi a yau za su doke Real Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.