An hada City da Barcelona
An hada Manchester City wasa da Barcelona kamar yadda aka hada kungiyoyi biyu a kakar da ta gabata, inda Barcelona ta yi waje da City da jimillar kwallaye ci 4-1 a zagaye na biyu a gasar Zakarun Turai. Haka ma an hada Paris Saint-Germain da Chelsea kamar yadda suka fafata a kakar da ta gabata inda a karawa ta farko PSG ta doke Chelsea amma kuma Chelsea ta rama a karawa ta biyu.
Wallafawa ranar:
An hada Bayer Leverkusen ne da Atletico Madrid
Juventus da Borussia Dortmund
Schalke 04 da Real Madrid mai rke da kofin gasar
Shakhtar Donetsk da Bayern Munich. Wannan ne karon farko da kungiyoyin biyu na Jamus da Ukraine za su gamu.
Kuma saboda rikici da ake yi a Ukraine an dauke wasan daga Donetsk zuwa Lviv garin da ke kusa da Poland.
Arsenal za ta fafata ne da Monaco. Basel da Porto.
A watan Fabrairu ne za’a fara fafatawar farko , sai a watan Maris a yi karawa ta biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu