Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

City ta kori Roma a Zakarun Turai

Manchester City ta shiga zagaye na biyu a gasar zakarun Turai bayan ta doke Roma ci 2 da 0. Samir Nasri ne ya taimakawa City tsallakewa wanda ya fara bude raga sannan ya mikawa Zabaleta kwallo ta biyu ya jefa a ragar Roma.

Samir Nasri wanda ya taimakawa Manchester City doke Roma a gasar Zakarun Turai
Samir Nasri wanda ya taimakawa Manchester City doke Roma a gasar Zakarun Turai REUTERS/Max Rossi
Talla

Wannan ne karo na 50 da Nasri ke haskawa a gasar Zakarun Turai.

A daya bangaren kuma Bayern Munich ta lallasa CSKA Moscow ci 3 da 0 ne, wanda ya ba kungiyar Roma nasarar shiga gasar Europa duk da ta sha kashi a hannun City.
Barcelona kuma ta kwace matsayi na farko a rukunin F bayan ta doke PSG ci 3 da 1.

Ibrahimovic ne ya fara jefa kwallo a ragar Barcelona amma daga bisani Messi ya farke kwallon sannan Neymar da Suarez suka jefa sauran kwallayen guda biyu a ragar PSG.

Schalke 04 ta Jamus tana cikin kungiyoyin da suka shiga zagaye na biyu bayan da doke Maribor ci 1-0.

Schalke 04 ta samu sassauci ne bayan Chelsea ta casa Sporting Lisbon ci 3 da 1.
Dukkanin kungiyoyin Jamus sun tsallake zuwa zagaye na biyu a gasar zakarun Turai, Schalke 04 da Bayern Munich da Dortmund da Bayer Leverkusen.

Athletic Bilbao ta doke Borisov ci 1 da 0, kamar yadda FC Porto ta sha kashi ci 1 da 0 a hannun Shakhtar Donetsk.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.