Isa ga babban shafi
Premier League

Sabuwar Rayuwar Manchester bayan zamanin Moyes

A Premier League ta Ingila ido zai koma ne a Old Trafford a karshen mako domin ganin yadda zata kaya da Ryan Giggs wanda ya gaji David Moyes da Manchester ta kora. Haka kuma babbar karawa tsakanin Liverpool da Chelsea da ke saman teburin Premiership.

Ryan Giggs na Manchester United
Ryan Giggs na Manchester United REUTERS/Darren Staples
Talla

A gobe Assabar ne Manchester United zata karbi bakuncin Norwich City, inda Ryan Giggs zai gwada sa’arsa a matsayin kocin United a karon farko bayan kungiyar ta raba gari da David Moyes wanda ya gaji Sir Alex Ferguson.

A ranar Lahadi ne kuma Liverpool da ke harin lashe kofin Premier a karon farko tun 1990, zata kece raini da Chelsea da ke bi mata a tebur

Tuni Mourinho yace zai ajiye wasu manyan ‘Yan wasan shi domin mayar da hankalinsa ga gasar Zakarun Turai.

Sai dai kuma matakin na Mourinho baraka ce ga Manchester City da ke fatar Chelsea ta doke Liverpool domin tana da kwanten wasa guda tsakaninta da Crystal Palace.
Maki shida ne ya raba Liverpool da City da ke matsayi na uku.

Arsenal kuma da ke yakin tsallakewa zuwa gasar zakarun Turai sai a ranar Litinin ne zata karbi bakuncin Newcastle United a Emirate.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.