Isa ga babban shafi
Premier League

Wasannin Premier sun yi wa Liverpool Kyau

Kungiyar Liverpool ta fara haramar lashe kofin gasar Premier ta Ingila bayan ta doke Norwich City ci 3-2 a jiya Lahadi, kuma yanzu tazarar maki 5 ne ta ba Chelsea da ta sha kashi a hannun Sunderland ci 2-1.

'Yan Wasan Kungiyar Liverpool suna murna
'Yan Wasan Kungiyar Liverpool suna murna REUTERS/Nigel Roddis
Talla

Liverpool tana harin lashe kofin gasar ne a karon farko tun a 1990. Kuma yanzu Liverpool ta buga wasanni 11 ba tare da samun galabarta ba a Premier.

Liverpool yanzu tana neman maki bakwai ne ta lashe kofin Premier, inda a karshen mako mai zuwa zata kece raini da Chelsea da suke hammaya.

Kungiyar Arsenal kuma ta doke Hull City ne ci 3-0, wacce zasu kuma kece raini da juna a gasar FA zagayen karshe.

Manchester United kuma ta sha kashi ne ci 2-0 a hannun Everton, a karawa ta farko tsakanin kungiyoyin biyu da Davis Moyes ya kai ziyara Goodison Park bayan ya gaji Sir Alex Ferguson.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.