Isa ga babban shafi
FIFA

Messi ya taya Cristiano murna

Lionel Messi na Barcelona ya taya abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo na Real Madrid murna wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya ta Ballon d’Or a 2013. Messi sau hudu yana lashe kyautar amma a bana Cristiano ya doke shi.

Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a wajen bikin zaben gwarzon dan wasan duniyaa Zurich
Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a wajen bikin zaben gwarzon dan wasan duniyaa Zurich REUTERS/Ruben Sprich
Talla

Franck Ribery na Faransa da ke taka kwallo a Bayern Munich shi ne ya zo a matsayi na uku.

Messi ya fahimci dalilin da ya sa Cristiano ya fashe da kuka a lokacin da aka bayyana sunansa a matsayin wanda ya lashe kyautar.

“Wannan lokaci ne na farin ciki” inji Messi yana mai cewa Cristiano ya cancanta ya lashe kyautar a bana.

An tambayi Messi yadda ya ji a ransa saboda bai lashe kyautar ba a bana, Dan wasan yace dukkaninsu sun taka rawa illa raunukan da ya samu a farkon kakar wasa.

Batun lashe Kyautar Gwarzon duniya da Cristiano ya yi, shi ne ya mamaye kanun labaran Jaridun kasar Spain inda 'yan wasan biyu ke taka kwallo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.