Messi ya fara jefa kwallaye a raga bayan ya murmure
Da wartsakewar Lionel Messi ya jefa wa Barcelona kwallaye biyu a daren Laraba bayan kwashe tsawon kwanaki 59 yana jinya, inda Barcelona ta lallasa Getafe ci 4-0 a gasar Copa Del Ray.
Wallafawa ranar:
An sako Messi ne a fili ana minti 63 da fara wasa wanda ya canji Andres Iniesta bayan tuni Cesc Fabregas ya jefa kwallaye biyu a raga.
Yanzu Dan wasan yana da jimillar kwallaye 16 a kakar bana.
Messi wanda ya kafa tarihin lashe kyautar Gwarzon duniya karo hudu yace yana fatar samun nasarori a 2014 kamar yadda Dan wasan ya shaidawa kafar Telebijin ta Barca.
Messi ya tabbatar da cewa zai kai ziyara Zurich a ranar Litinin inda za’a gudanar da bikin karrama gwarzon dan wasan duniya a bana.
Sau bakwai ken an a jere Messi yana shiga sahun mutane uku da ake zaben gwarzon duniya amma dan wasan yace lashe kyautar a karo na biyar ba damuwar shi ba ne.
A ranar Assabar ne dai za’a barje gumi tsakanin Barcelona da Altelitico Madrid da ke hammaya a teburin La liga.
Real Madrid dai zata yi fatar su kashe kansu da kunnen doki ko a tashi wasa babu ci don su yi barin maki biyu. A yau Alhamis ne Real Madrid zata fafata da Osasuna a gasar Copa de Ray.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu