Isa ga babban shafi
FIFA

Tawagar FIFA zasu kai ziyara Brazil

A karshen watan Afrilu ne ake sa ran tawagar hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA zasu kai ziyara kasar Brazil domin gane ma idonsu tare da tantance filayen wasanni da za’a gudanar da gasar cin kofin Duniya a shekarar 2014.

Jérôme Valcke Jami'in Hukumar FIFA wanda zai jagoranci tawaga zuwa Brazil
Jérôme Valcke Jami'in Hukumar FIFA wanda zai jagoranci tawaga zuwa Brazil DR
Talla

Ricardo Babban Directan kwamitin gasar yace tawagar ta FIFA zasu kawo ziyara ne a ranar 25 ga watan Afrilu domin diba filayen wasannin a biranen Rio de Janeiro da Brasilia da Salvador.

Gasar Confederation da za’a gudanar a kasar zata kasance gasar share fage a kasar kafin gudanar da gasar cin kofin duniya a shekarar 2014.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.