Hatsarin jirgi mai saukar ungulu ya kashe mutane 5 a Cuba
Mutane 5 sun mutu a Cuba, bayan da jirgi mai saukar ungulu da suke ciki ya rikito lokacin da ya taso daga lardin Holguin zuwa gabashin tsibirin Guantanamo, kamar yadda ma’aikatar tsaron kasar ta sanar.
Wallafawa ranar:
Wata sanarwa dag ma’aikatar ta ce jirgin ya fadi a wani tsauni ne, kuma ilahirin wadanda ke cikin jirgin sun ce ‘ga garinku nan’.
Sanarwar ta ci gaba da cewa ma’aikatar ta kafa wani kwamitin bincike da zummar gano musabbabin hatsarin, sai dai ba ta yi wani karin bayani a game da ko su wanene ke cikin jirgin ba.
A shekarra 2018 ne wani hadarin jirgin sama mai muni ya auku a Cuba, inda wani jirgi ya fadi jim kadan bayan ya bar filin tashi da saukar jiragen sama na Havana, lamarin da ya lakume rayuka 112, yayin da mutum guda ya tsira.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu