Isa ga babban shafi

Hari da wuka ya hallaka mutane 3 a Scotland

Rahotanni daga Glasgow dake Scotland sun ce akalla mutane 3 suka mutu lokacin da wani ya dabawa mutane wuka a wani otel, yayin da jami’an tsaro suka harbe shi har lahira.

Inda wani yakai hari da wuka a Glasgow, na kasar Scortland ranar 26 ga watan Yuni 2020
Inda wani yakai hari da wuka a Glasgow, na kasar Scortland ranar 26 ga watan Yuni 2020 @JATV_SCOTLAND/via REUTERS
Talla

Rundunar Yan Sandan Scotland ta tababtar da cewar jami’in ta guda na daga cikin wadanda aka dabawa wukar, yayin da Yan Sanda dauke da makamai yanzu haka ke gudanar da bincike a unguwar.

Jagorar Yankin Nicola Sturgeon ta bayyana kaduwa da lamarin, yayin da Yan Sanda ke mata bayanin abinda ke faruwa akai akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.