Isa ga babban shafi
Turai

Guguwar Irma ta halaka sama da mutum 40

Hukumomi a Cuba sun bada sanarwar mutuwar mutane 10 yau bayan isar guguwar Irma cikin karshen makon nan wadda ta raba da dama da muhallinsu baya ga lalata muhimman wurare. Sanarwar hukumomin dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da guguwar ke ci gaba da ratsa sassa daban-daban na duniya cikin kasa da mako guda.

Mummunar guguwar ta Irma hade da ambaliyar ruwa ta tilasta kwashe mutane da dama daga yankunan data afkawa, baya ga halaka mutane da ma sabbaba asarar dukiya mai tarin yawa.
Mummunar guguwar ta Irma hade da ambaliyar ruwa ta tilasta kwashe mutane da dama daga yankunan data afkawa, baya ga halaka mutane da ma sabbaba asarar dukiya mai tarin yawa. Reuters
Talla

Adadin wadanda aka tabbatar da mutuwarsu sanadiyyar guguwar ta Irma ya karu zuwa sama da 40, inda a tsibirin St Barts da na Saints Martin da ke Faransa da kuma wani yanki na Dutch kadai mutum 14 suka mutu.

Sai kuma tsibirin Carebbean da ke Birtaniya inda mutum 6 suka mutu yayinda a Virgin Island na Amurka kuma mutum 4 sai kuma mutum 2 a Puerto Rico da kuma mutum daya a Barbuda.

Haka kuma akwai mutum 3 da suka mutu sakamaon hadarin motar da guguwar ta haddasa a Florida.

A bangare guda kuma a yau ne sarki Willem-Alexander na Holland zai kai ziyara wasu yankunan tsibirin Caribbean don ganewa idonsa irin bannar da guguwar Irma ta tafka a wajen.

Yayin ziyarar wadda zai gudanar tare da rakiyar ministan cikin gida Ronald Plasterk, sarkin zai gana da jami’an da ke aikin bayar da dauki da ma jami’an tsaron da ke kula da wajen, baya da guguwar ta lalata filin jirgin saman Princess Juliana da asibiti da kuma makaranta.

Miliyoyin mutane ne dai suka rasa matsugunan su inda a Amurka kadai aka kwashe sama da mutum milyan guda da guguwar ta shafi yankunansu, wanda kuma shi ne mafi yawan mutane da aka taba kwashewa a tarihin annobar da ke afkawa kasar.

har yanzu dai ba'a kammala kididdige mutanen da suka mutu ba duk da cewa wasu na ganin al'amura sun fara dai dai a wasu yankuna da lamarin ya faru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.