Isa ga babban shafi

Nijar ta tabbatar da mutuwar mutane 11 a harin da 'yan ta'adda suka kai

Akalla mutane 11 ne aka kashe a hare-haren da ake kyautata zaton masu ikirarin jihadi ne suka kai a karshen mako a wasu kauyuka biyu da ke kusa da iyakar Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso, kamar yadda ma'aikatar tsaron Nijar ta sanar.

Shugaban majalisar soji ta Nijar Janar Abdourahmane Tiani.
Shugaban majalisar soji ta Nijar Janar Abdourahmane Tiani. REUTERS - STRINGER
Talla

Harin dai ya zo ne a daidai lokacin da jami'an tsaro Nijar a ranar Juma'a suka kai hare-hare ta sama da kuma ta kasa, wanda ma'aikatar ta ce ya lalata hanyoyon sadarwar 'yan ta'addan.

Sanarwar ta kara da cewa soja daya ya rasa ransa yayin da biyar suka samu raunuka a ranar ta Juma’a, bayan da motar da su ke sintiri ta taka wata nakiya a Ouro Gueladjo mai tazarar kilomita 70 daga Niamey babban birnin kasar.

A ranar 17 ga watan Disambar daya gabata, shugaban mulkin sojan kasar Janar Abdourahamane Tiani, ya ce kasar na ci gaba da daidaita al'amuran tsaro, yana mai cewa sojojin sun samu nasara da dama wajen yaki da ‘yan ta’adda.

Majiyoyin soji da na al’ummar yankin sun ce a ‘yan makonnin da suka gabata, an samu kwanciyar hankali a yankin da ke kan iyaka da Burkina Faso da Mali, ganin yadda a baya ya fuskanci hare-haren mayakan da ke ikirarin jihadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.