Isa ga babban shafi

Sojojin Nijar na son kulla yarjejeniya da sojojinTurai

Bayan da suka bukaci ficewar sojojin kasar Faransa dubu 1 da 500  daga Jamhuriyar Nijar, sabbin mahukuntan birnin Yamai da suka kifar da gwamnatin Mohamed Bazom a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata,  sun bayyana aniyar sake tattauna yarjejeniyar soji tare da kasashen da suka jibge dakarunsu a kasar, abin da ke nufin cewa har yanzu ba su rufe kofar tattaunawar kasancewar dakarun ketare a kasar ba. 

Shugaban mulkin sojin Nijar , Abdourahmane Tchiani.
Shugaban mulkin sojin Nijar , Abdourahmane Tchiani. AP
Talla

A cikin wata  wasika da  Ofishin Harakokin Wajen Nijar ya aika wa jami’an diflomasiyar kasashen ketare, kasar ta bayyana aniyar sake duba yarjeniyoyin sojin da ta kulla a baya da aminan huldarta, da suke da sojoji yanzu haka, sai dai ba a zana sunayen kasshen da ke da sojojin ba. 

Kasashen Amurka da Jamus tuni sun bayyana fatan ganin an bar su sun ci gaba da barin sojojinsu a kasar inda Amurka ke da sojoji 1da 300 a yayin da Jamus ke da sojoji 100.

A makon da ya gabata Ministan Tsaron kasar Jamus da ya ziyarci Jamhuriyar Nijar ya bayyana fatan ganin mahukuntan mulkin sojin na Nijar sun bar sojojin kasarsa 100 da ke da sansani a Tilia da ke cikin jihar Tahaoua domin ci gaba da horar da sojojin na Nijar.

Kasashen Belgium da  Italiya da sauran kasshen Turai su ma na da sojoji a Jamhuriyar ta Nijar a karakashin shirin  EUCAP Sahel na kungiyar Tarayyar Turai.

A cewar Ma’aikatar Wajen kasar ta Nijar za a sake mika wa wadannan kasashe wata sabuwar yarjejeniya da za ta tafi a kan wata sabuwar turbar huldar kasa da kasa.

Tun bayan zuwa sojoji kan karagar mulkin Nijar a karkashin majalisar  (CNSP), sabbin mahukuntan ke cike da fatan ganin sun tabbatar da sake dawowar cikakken 'yancin da kasar ke da shi tare da kare muradunta. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.