Isa ga babban shafi

Jihohin Najeriya 31 za su fuskanci ibtila'in ambaliyar ruwa a bana

Ma’aikatar albarkatun ruwa a Najeriya ta yi gargadin yiwuwar fuskantar ambaliya a kananan hukumomin kasar 148 da ke jihohi 31 yayin damunar shekarar nan ta 2024.

Ko a bara ambaliyar ruwa ta haddasa mummunar illa a sassan Najeriya.
Ko a bara ambaliyar ruwa ta haddasa mummunar illa a sassan Najeriya. REUTERS - FEISAL OMAR
Talla

Ministan ruwa na Najeriyar Farfesa Joseph Utsev da ya ke kaddamar da dabarun tunkarar matsalar ambaliyar ruwa yayin bikin da ya gudana a Abuja, ya ce jihohin Kano da Katsina da kuma Kwara na sahun gaba wajen yiwuwar fsukantar ambaliyar.

Baya ga jihohin 3 a cewar ministan akwai kuma wasu jihohi 28 wadanda ya zama wajibi su dauki matakan kariya don dakile barnar da ambaliyar ka iya yi a lokacin zubar ruwan saman.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriyar NAN ya ruwaito cewa hasashen kuma da ke nazartar yanayin zubar ruwan sama ta kasar ya nuna jihohi 31 da matsalar ta ambaliya za ta tsananta.

Hasashen hukumar ya nuna jihohin na Adamawa da  Akwa-Ibom da Anambra baya ga Bauchi da Bayelsa da kuma Benue sai jihar Borno a matsayin wadanda ambaliyar za ta tsananta.

Sauran jihohin a cewar hasashen akwai Cross-River da Delta da Ebonyi ka na Edo da Imo da Jigawa da Kaduna sai Kano da Katsina da Kebbi sannan Kogi.

Haka zalika akwai jihohin Kwara da Lagos da Nasarawa da Neja sannan Ogun da Ondo da Osun da kuma Oyo sannan Plateau da Rivers da Sokoto da Taraba da Yobe wadanda za su gamu da ambaliyar a bana.

Mr Utsev ya roki al’ummar Najeriya su dauki matakan kariya daga ibtila’in na ambaliyar ruwa don kaucewa makamanciyar asarar da kasar ta gani a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.